21 Janairu 2021 - 18:05
Iran : Dole Amurka Da Faransa Su Daina Tura Makammai A Gabas Ta Tsakiya

Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bukaci Amurka da kasashen yamma su kawo karshen ciniki da bada makamai ga kasashen gabas ta tsakiya.

ABNA24 : Wannan bayyanin ya fito ne a ta bakin ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawwad Zarif, wanda ke cewa idan har da gaske Amurka da kasashen yamma su ke kan batun makamai, to dale ne sai sun dakatar da ciniki da kuma baiwa kasashen gabas ta tsakiyya makamai.

Mista, Zarif, ya ce kasashen musamman Amurka da Faransa, sun yi kaurin suna wajen ciniki da mika makamai na bilyoyin daloli ga kasashen gabas ta tsakiyya, wanda kuma ake yakar al’ummar Falasdinu da Yemen dasu.

Kashi 25 cikin dari na makamman duniya ana shiga dasu ne ko kuma sayar dasu a gabas ta tsakiya inji ministan harkokin wajen kasar ta Iran.

A hannun daya kuma da yake amsa tambaya game da takaddamar Amurka da Iran akan yarjejeniyar nukiliyar Iran, M. Zarif, ya sake nanata cewa babu bukatar sake tattaunawa kan yarjejeniyar, abunda ya faru shi ne Amurka ce ta kasa cika alkawuran data dauka, kuma a cewarsa kamar yadda jagoran juyin juya halin musulinci na kasar ya fada, idan Amurka ta dage takunkuman data kakaba, babu matsala, Iran ita ma zata mutunta yarjejeniyar.

342/